Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Shugaban sashin tsaro a ma'aikatar aikin hajji da umrah Mohammad Al-Qarni ya sanar da halartar mahajjata miliyan biyu da dubu 50.
Ya yi bayanin dangane da haka: An fara aiko da maniyyata ne a jiya da yamma kuma za a ci gaba da aikewa da alhazai har zuwa karfe 10:00 na safe a ranar Litinin (8 ga watan Zul-Hijjah) domin kowa ya shiga Mina a lokacin da aka kayyade.